Tinubu ya yaba wa gwamnonin Najeriya bisa amincewa da ƙudurin haraji
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa ƙungiyar gwamnonin Najeriya saboda amincewar da suka yi da ƙudurin yin gyara ga dokar haraji, wanda a yanzu ke gaban majalisar dokokin tarayya, domin neman amincewa.
BBC ta rawaito cewa, cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan yaɗa labarai da tsare tsare, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya jinjina wa gwamnonin kan sadaukarwarsu, wadda za ta samar da haɗin kai tsakanin shugabanni a faɗin ƙasar, ba tare da la'akari da ɓangaranci ko ƙabilanci ko kuma na siyasa ba.
Tinubu ya bayyana cewa babbar manufar sabon ƙudurin dokar harajin ita ce "taimaka wa talaka, da bunƙasa gasa a fannin tattalin arziƙi, da kuma janyo hankalin masu zuba jari na cikin gida da kuma ƙasashen waje.
A cikin sanarwar, Tinubu ya ce sabunta dokar harajin ƙasar, wadda tuni aka daina yayin ta abu ne mai muhimmanci.
A ranar Alhamis ne gwamnonin Najeriya suka amince da ƙudurin dokar harajin bayan sun yi mata wasu ƴan gyare-gyare.
Dokar, wadda shugaba Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dokokin Najeriya ta haifar da zazzafar muhawara, lamarin da ya kai ga jinkirin amincewa da ita.
Tun farko, gwamnoni da dattaijan yankin arewacin ƙasar sun yi watsi da ƙudurin, inda suka bayyana shi a matsayin wanda zai cutar da al'umma.
Daga baya shugaban ƙasar ya buƙaci ma'aikatar shari'a ta ƙasar ta yi aiki tare da Majalisar Dokoki domin warware matsalolin da suka janyo cece-ku-ce a kan dokar.
Yanzu dai Tinubu ya buƙaci majalisar dokokin tarayya ƙasar ta hanzarta tattaunwa kan ƙudirin harajin domin amincewa da shi.