Duk da saukar farashin fulawa ba za mu rage farashin burodi ba sai dai mu ƙara girman sa~ Masu gashi a Kano
Ƙungiyar masu gasa burodi da kayan fulawa ta ƙasa, reshen jihar Kano, ta ce ba za ta iya rage farashin burodi ba sai dai ta ƙara girman sa akan farashin sa na yanzu.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwar bayan taro da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta fitar a yau Laraba, bayan ganawa da kungiyar masu gashin burodi.
A cewar sanarwar, kungiyar ta nuna cewa duk da an samu ragi sosai na farashin fulawa, amma farashin man gyada, da suga da itace da sauransu, wadanda su ke su ne manya-manyan sinadaran yin burodi, har yanzu farashin su bai sauka ba.
Sanarwar tace masu gasa burodin sun amince ba za su rage farashin burodi ba, amma za su kara masa girma da kauri.
Haka zalika, a sanarwar Bayan taron, wacce shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin-Gado da Shugaba da Sakataren kungiyar su ka sanyawa hannu na hadin gwiwa, sun kira ga kamfanonin fulawa da su kara ragi na sama da naira dubu 2 kan buhu guda, musamman don ƙaratowar azumin watan Ramadan.
Sun kuma yaba da kokarin kamfanonin na rage farashin fulawa daga sama da Naira Dubu 80 zuwa kasa da Naira dubu 60.