Gamayyar kungiyoyin matasa na farar hula 87 ne suka nuna goyon bayansu ga Gwamnatin Kano domin tantancewa
Kungiyoyin matasa na farar hula 87 sunyi taron manema labarai domin nuna gasuwarsu ga Gwamnatin Jihar Kano na tsaftace kungiyoyi bata gari.
Taron ya gudana ne karkashin jagorancin kungiyar youths mobilization by media dake gida zamanta a gidan zoo, daya ke karin haske Salisu Gambo Detol yace gamayyar kungiyoyin sun amince tare da goyon baya gwamnatin Kano domin kafa kwamatin da zai bibiyi dukkanin kungiyoyin farar hula dake Jihar.
Domin tantancesu da tsaftace domin kare mutuncin jihar da addinin ta dama al'ummar jihar baki daya, yace bazasu amince da wasu manyan kungiyoyi da za'ai amfani dasu wajen rusa tarbiyyar al'umma da al'adunsu ta wajen auran jinsi, daukar nauyin ta'addanci, kaucewa tarbiyya dama ire-iren dangoginsu.
Inda yace suna goyon baya Dari bisa Dari da wannan gyara da Gwamnatin Kano zatayi, sannan suna barranta kansu da wasu kungiyoyi da sukace basu amince da kwamatin da Gwamnatin zatayi ba,
Ya kara da cewar Gwamnatin Kano nada damar da zatayi kwamati domin gano ire-iren bata garin kungiyoyi da suke narkewa da kungiyoyin da ake amfani dasu ana tura musu makudan kudade domin a rusa al'ummar kasa da Jihar Kano baki daya.