Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da shugaban ma’aikata na riko, kuma babban sakatare, Salisu Mustapha, bisa zargin da ake na zabtare wa ma’aikata albashi da kuma rashin biyan wasu ma'aikatan su.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Dawakin-Tofa ya fitar a jiya Alhamis, ta kuma umurci Mustapha da ya ajiye mukaminsa na babban sakatare a karkashin ofishin shugaban ma’aikata, domin ba da damar gudanar da bincike ba tare da tangarda ba.
Domin tabbatar da ci gaba da gudanar da aikin gwamnati, gwamnan ya amince da nadin Umar Jalo, babban sakatare a bangaren REPA, a matsayin sabon shugaban ma’aikata na riko, har sai an kammala binciken da ake yi.
Gwamnan ya kara jaddada matsayinsa na yaƙi da cin hanci da rashawa, ya na mai gargadin cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci mai tsauri.
Kwamitin binciken da gwamnan ya kafa, karkashin Abdulkadir Abdussalam, an ba shi wa’adin kwanaki bakwai don gano tushen kura-kuran da aka yi tare da gabatar da sakamakon binciken.
An nada Mustapha ne a matsayin shugaban ma’aikata a farkon wannan watan bayan hutun jinya da aka baiwa shugaban ma’aikata na dindindin, Abdullahi Musa, wanda yanzu haka yake jinya a kasar Indiya.