Gwamnatin Najeriya za ta kafa rundunar
tsaron layukan wutar lantarki
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta kafa wata runduna ta musamman domin kare layuka da cibiyoyin samar da wutar lantarkin ƙasar daga ɓat-gari masu sace kayyakin wutar.
BBC ta rawaito cewa , Ministan cikin gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana haka ranar Juma'a a wata hira da gidan talbijin na Channels da ke ƙasar.
Mista Tunji-Ojo ya ce sun ɗauki mataki tare da takwaransa na wutar lantarki, domin saman da abin da ya kira ''dakarun tsaron lantarki'' na ƙasa.
Ya ƙara da cewa za a samar da dakarun ne daga rundunar tsaron fararen hula ta Civil Defence, kuma za a ɗora musu alhakin dakatar da lalata abubuwan lantarkin, lamarin da ke haifar da katsewar wutar a wasu lokuta a faɗin ƙasar.
A baya-bayan nan dai ƙasar na yawan fama da katsewar lantarkin, sakamakon abin da hukumomin ƙasar suka ce sace wasu wayoyin da ɓata-gari suke yi ne ke haifarwa.
Ministan cikin gidan ya ce lokaci yayi da ya kamata a É—auki matakin bai É—aya domin magance matsalar.