Hukumar tace fina-finai ta gargadi masu gidajen Gala da sauran guraren wasanni a Jahar Kano dasu rufe har zuwa lokacin da zata sanar da budewa
Cikin wata takarda da yasanyawa hannu jami'in hulda da jama'a na hukumar tace fina-finan na Jihar Kano Abdullahi Sani Sulaiman yace, Blbiyo bayan karatowar wata mai falala na Azumin Ramadana, Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab'i ta Jahar Kano, Alh Abba El-mustapha ya bada umarnin rufe dukkannin gidajen Gala da sauran guraren wasanni a Jahar Kano har zuwa kammala ibadar ta Azumin.
Da yake jawabi a yayin kafa wani kwamitin na karta kwana karkashin jagorancin Mal. Nasiru (Shehi), ya ce aikin wannan kwamitin shine ya tabbatar da babu wani gidan wasa a Jahar Kano da suke gudanar da wasa a lokacin Azumi a yayin da Abba El-mustapha yasha alwashin yin hukunci mai tsauri ga duk mai gidan wasan da aka sami gidansa da karya wannan doka.
Haka kuma wannan umarnin ya hada hana dukkannin yan wasa zama a gidajen wasanninsu tsawon wannan lokaci na Azumi har zuwa kammala Ramadana.
A karshe ya yi kira ga Kungiyar masu gidajen wasannin ta Gala dasu saka ido sosai ga ya'yan Kungiyar tasu domin tabbatar da sun yi biyayya ga wannnan sabon umarnin.
Abba El-mustapha ya kuma godewa malamai tare da al'ummar Jahar Kano dangane da shawarar da suke ba shi tare da nuna goyan bayansu a gareshe tsawon lokaci tun fara aikinsa a matsayin sabon Shugaban Hukumar ta tace fina-finai a Jahar Kano.