Jama'atu Nasril Islam ta nemi haɗin kai da daidaito a tsakanin malaman addinin Musulunci bisa gabatowar azumin watan Ramadan.
Jama'atu Nasril Islam ta nemi haɗin kai da daidaito a tsakanin malaman addinin Musulunci bisa gabatowar azumin watan Ramadan.
kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta jaddada bukatar hadin kai da daidaito a tsakanin malaman addinin Musulunci gabanin zuwan watan azumin Ramadan.
Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bayyana hakan a wajen taron shekara shekara da aka saba yi kafin watan Ramadan da aka gudanar a Kaduna.
Sarkin Musulmi ya ce, dole ne a hada kan Musulmi a karkashin inuwa daya duk da ana iya samun bambance bambance, amma akwai bukatar samun daidaito a tsakani, kuma wannan ya zama wajibi a wannan bangare.
Ya kara da cewa bai kamata a bar bambance bambancen da ke tsakanin da fahimta ya raba kan musulmi har ta kai ga zagin juna ba,duk yadda malami yakai ga sani tabbas akwai wanda ya fishi sani.
Sarkin Musulmi ya ce ta hanyar bin ka’idoji da dabi'a mai kyau ne kadai, malamai za su iya inganta kyakkyawar koyarwa da bayar da ilimi a watan Ramadan ga kowa da kowa