Majalisar Malaman ta Jihar Kano ta yanke hukuncin kan rikicin masallacin Sheikh Bin Uthman (Sahaba) dake kundila.
Shugaban majalisar malamai ta Kano Sheik Ibrahim Khalil ya bayyana cewa bayan zama da dukkanin bangarorin da danbarwar Sabon masallacin Sahaba dake kundila, majalisar ta yanke hukuncin na karshe a kan dambarwar.
” Mun yanke hukuncin Sheikh Muhammad Bn Othman zai koma masallacinsa na Sahaba , shi kuma mai kifi da sauran mutanensa za su cigaba da rike na su masallacin na jami’urrahman”.
Malam Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne lokacin da yake bayyana sakamakon zaman da suka yi ga manema labarai a Kano.
Ya ce Sheikh Muhammad Bn Othman ya Amince zai cigaba da jagorantar sallah a tsohon masallacinsa na Sahaba dake kundila, yayin da su kuma su mai kifi za su cigaba da gudanar da harkokin masallacinsu na jami’urrahman.