Majalisar Wakilai za ta gudanar da taron jin ra’ayi na jama’a kan kudirorin gyaran haraji a ranar 26 ga Fabrairu.
Kakakin majalisa, Tajudeen Abbas, ya sanar hakan yayin zaman majalisar na ranar Talata inda ya ce za a shirya taron jin ra’ayi don tattara ra’ayoyi daga al’umma.
Domin cimma wannan buri, majalisar ta kafa kwamitin musamman mai mambobi 36 da ke da alhakin tsara zaman. Wannan kwamiti zai hada da kwararru a fannin gudanar da haraji, inda za a mayar da hankali kan fa’idodin da gyaran harajin zai kawo.
A cewar Kakakin Majalisa Abbas, Abiodun Faleke zai shugabanci kwamitin, yayin da Seidu Abdullahi, mataimakin shugaban kwamitin kudi na majalisa, zai zama mataimakinsa.
Sauran mambobi sun hada da Alhassan Ado-Doguwa, Nicholas Mutu, Fred Agedi, da Idu Igariwey, tare da wasu 'yan majalisar.