Kungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ta ayyana shiga yajin aiki na sai baba-ta-gani daga ranar 18 ga watan Fabrairu, sakamakon rashin warware batutuwan da suka shafi walwalar ma’aikata.
Kungiyar ta sanar da wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da shugabanta, Dakta Peter Adamu, da sakatarenta, Dakta Peter Waziri, suka sanya wa hannu, kuma suka aikawa Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) a Kaduna ranar Talata.
Sanarwar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan amincewar kwamitin zartarwa na kasa na ASUU.
"Kungiyar Malaman Jami’a, reshen KASU, na son sanar da jama’a cewa kwamitin zartarwa na kasa ya amince da bukatar reshen jami’ar don shiga yajin aiki kuma na sai baba-ta-gani daga yau, 18 ga Fabrairu, 2025.