Karamin Ministan Gidaje da Raya Burane, Yusuf Abdullahi Ata ya ce matukar aka sake baiwa Abdullahi Abbas ko irinsa Shugabancin jam’iyyar APC a jihar Kano sai sun fice daga jam’iyyar.
Ata ya yi wannan barazana ne a wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC, reshen Karamar Hukumar Fagge, inda ya fito, s jiya Asabar.
“Mu na gaya wa kowa indai aka mayar da su billahillazi duk irin mu fita za mu yi kuma sai jam’iyyar ta sake faduwa. Irin wadannan mutanen ba ma tare da su kuma ko me za a yi mu bama tare da su, su na aiko mana da sako mu ma mu na aika musu da sako," in ji shi.
Ya ce irin kalaman da Abdullahi Abbas ya yi na tuhumar Allah da izgili su ne su ka kayar da jam’iyyar APC a zaben 2023 , kuma ya ce muddin aka sake baiwa Abdullahi Abbas shugabancin APC a Kano ba makawa sai jam’iyyar ta sake faduwa.
” Mu an yi mana tarbiyya mun san waye Allah, mun san waye malami mun kuma san waye babba, saboda haka ba za mu sauka daga tarbiyyar mu ba, in aka kuma sa su za mu fita kuma wallahi jam’iyyar sai ta sake faduwa”. Inji Ministan
Yusuf Abdullahi Ata ya ce dole ne a chanza su Abdullahi Abbas a kawo mutanen kirki masu mutunci , saboda Allah ya sake baiwa APC mulkin jihar Kano, domin Allah ya shi yake ba da mulki ba yawan kuri’a ba.
“Kuri’a ba ta ba da mulki ba, kudi ba zai ba ka mulkin ba , al’umma ba za su ba ka mulki ba , ai an zabi Gawuna da Garo kuma su suka ci zabe clean, amma Allah ya ba da dama aka yi mana magudi kuma mu ka je kotu aka tantance aka gano an yi mana magudi, amma daga karshe mai bayarwar sai ya hana mu saboda mun kalubalance shi”. A cewar Ata