Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya bayyana cewa kwamitin koli na jam'iyyar, Æ™arÆ™ashin jagorancin sa, ya gaji bashin Naira Naira biliyan 8.9.
Ganduje ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake magana a taron zartarwa na kasa na jam’iyyar APC.
A cewarsa, bashin ya taru ne sakamakon harkokin Shari'a kafin zaÉ“e da shari’o’in zabe, da kuma kararrakin zaben ‘yan majalisa, gwamna, da shugaban kasa.
Sai dai ya bayyana cewa Farfesa Abdul Kareem Kana (SAN), mai baiwa APC shawara kan shari’a na kasa, ya dukufa wajen ganin an rage bashin.
"Har yanzu muna kira ga kwamitin zartarwa na kasa da ya yi duba a kan haka,” in ji shi.