Rikici ya dabaibaye majalisar dokokin jihar Benue kan tsige Alkalin Alkalai na nihar, Mai shari’a Maurice Ikpambase, inda ya yi kamari a yau Laraba bayan da majalisar ta dakatar da ‘yan majalisa 13 saboda nuna adawa da matakin da aka dauka na masu rinjaye.
Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa jim kadan bayan da wakilai 23 daga cikin 31 su ka kada kuri’ar tsige Ikpambase, ‘yan majalisar 13 da ke adawa da matakin sun gudanar da taron manema labarai a Makurdi, inda suka yi Allah-wadai da matakin da kuma zargin an saba wa ka’ida.
Da ya ke mayar da martani, shugaban majalisar, Cif Hyacinth Aondona Dajoh, a yau Laraba ya ba da sanarwar dakatar da 'yan majalisar na tsawon watanni uku, yana mai zarginsu da aikata "ayyukan rashin mutunci da ke iya haifar da rikici a majalisar."
An kuma umurci mambobin da aka dakatar da su dawo da kudaden da aka ware musu a baya don yin balaguro zuwa ƙasar waje kuma ba za su yi tafiyar ba.