Shugaban Jami'iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas da Fa'izu Alfindiki sun bukaci kotu tayi watsi da karar da aka shigar gabanta
Shugaban Jami'iyyar APC a Kano Abdullahi Abbas Sanusi da tsohon shugaban karamar hukumar birni a zamanin mulkin Abdallahi Ganduje, Hon Fa'izu Alfindiki sun bukaci kotun shari'ar muslunci ta kasuwa da fatali da karar da aka shigar gabanta,
Kan zargin su da kalaman batanci da cin zarafin Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf, wanda sukace kotun bata da hurumin sauraron shari'ar.
Abdullahi Abbas da Faizu Alfindiki, sun bayyana haka ne ta bakin lauyan da ya tsaya a gaban kotun domin kare su, Barista Ismail Abdulaziz, inda yace bangaren masu kara basu fayyace abinda suke tuhumar wadanda yake karewa ba, a saboda haka yake rokon kotun ta duba ta gani, idan bata da hurumi kawai ta kori karar.
To sai dai lauyan masu kara, Barista Shazali Muhammad Ashiru, ya nemi Kotu ta bashi wata rana domin martani akan bukatar bangaren wadanda ake kara, inda daga nan ne kotun ta dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2025.