A gaggauta dakatar da ƙarin kuɗin wutar lantarki don ba za mu lamunta ba ~ NLC
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki da masu amfani da layin A da B da C.
Shafin intanet na tashar Channels ya ruwaito daga sanarwa da NLC ɗin ta fitar a ranar Lahadin data gabata,bayan wani taro da ta yi a jihar Adamawa.
"NLC ba ta amince da yunƙurin hukumar lantarki ta Najeriya NERC na ƙoƙarin sauya layin lantarki kwastomomi daga layin B da A da sunan haɓaka samun lantarki, alhali kuma yunƙuri ne kawai na ƙara wa mutane kuɗin wuta ba tare da sun shirya ba," in ji sanarwar.
"A fili yake dai yanzu masu ƙarfi a ƙasar na ƙara jefa marasa ƙarfi cikin ƙunci ta hanyar ƙara kuɗin haraji da lantarki da sauransu a daidai lokacin da tattalin arzikin ƙasar ya tsaya cak."