A Zauna Lafiya da Hakuri Kan Rikicin Masarautar Kano ~ Dan Siyasa Inuwa Waya Ga Sarki Aminu Ado Bayero na 15
Fitaccen dan siyasa a Kano, Inuwa Waya, ya rubuta wata budaddiyar wasika ga Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, yana mai kira gare shi da ya yi hakuri kuma ya fifita zaman lafiya a rikicin da ake yi kan masarautar Kano.
Waya ya jinjinawa Sarkin bisa shawarar da ya yanke na soke Hawan Sallah, yana mai cewa hakan ya dace duba da barazanar tsaro. Ya kuma yaba da halayen Sarkin na natsuwa da sanin ya kamata, waÉ—anda ya gada daga mahaifinsa marigayi Sarki Ado Bayero.
Ya tuna irin ƙalubalen da sarakuna suka fuskanta a baya, ciki har da yunkurin kisan gilla da cin zarafi na siyasa, yana mai jaddada cewa shugabanci na gaskiya yana buƙatar juriya da yarda da kaddara.
Duk da cewa yana da damar shari’a don Æ™alubalantar sauke shi daga sarauta, Waya ya shawarci Bayero da ya guji duk wani abu da zai iya haddasa tashin hankali ko rikici a Kano. Ya bukace shi da ya dogara ga tsarin shari’a kuma ya amince da hukuncin kotu a matsayin kaddarar Allah.
"Shugabanci ba wai iko kawai ba ne, yana da nasaba da haÉ—in kai, ci gaba, da zaman lafiya," a cewar Waya,
Yana mai kira ga Sarkin da ya mai da hankali kan cigaban Kano da habɓakar tattalin arziki.
Ya kammala da addu’ar zaman lafiya da shiriya daga Allah ga Sarkin da al’ummar Kano baki É—aya.