Allah ya yiwa fitaccen attajiri a Kano Alhaji Nasiru Ahali Rasuwa
Alhaji Nasiru Ahali, ya rasu a daren jiya Alhamis, bayan fama da jinya kamar yadda É—ansa, Aminu Ahali, ya sanar.
Marigayin mai shekara 108, shi ne shugaban kamfanin Mainsara & Sons, yana gudanar da harkar kasuwanci daban-daban, ciki har da buga littattafai da shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje da kwangila da gina gidaje da aikin sarrafa ƙarfe da sauransu.
Anyi jana'izarsa a masallacin Jumu’a na Nasiru Ahali da ke Kurnar Asabe da Æ™arfe 1 na rana a yau Juma’a.