Allah ya yiwa kwararren dan jarida me daukar hoto, Malam Zubairu Shaba rasuwa.
Ya rasu a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano bayan fama da rashin lafiya.
Malam Shaba ya yi aiki da jaridun New Nigeria, Triumph Hotline Magazine Daily Trust, Market Magazine da sauran jaridu.
Ya rasu ya bar mata É—aya da Æ´aÆ´a 13 da jikoki kuma tuni aka yi jana'izarsa a gidansa da ke unguwar Shagari Quaters a jihar Kano.
Muna addu'ar Allah ya gafarta masa.