Al’ummar Garin ‘Danzaki sunyi kira ga Gwamnan kano da ya kawo musu dauki kan wani aiki da za’a yi musu a Makabarta, makaranta da Gonakinsu ba bisa ka’ida ba
Mutanen yankin Dan zaki sun wayi gari da gannin wani kamfani ya fara gudanar da wani aikin wata hanya, wacce zata tafi har zuwa Garin Dawanau dake cikin karamar hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano.
Al’ummar Garin ‘Danzaki dake cikin karamar hukumar Gezawa sunyi kira ga Maigirma Zababben Gwamnan kano, Alh. Abba Kabir Yusuf da ya kawo musu dauki, akan wani aiki da ya biyo ta cikin Makabarta, ya hada da makaranta da kuma Gonakin jama’ar garin na ‘Danzaki.
Inda suka ce, da farko an fitar da inda za’ayi aikin a gurin da bai shafi gidajen Talakawan gari ko Gonakin su ba, daga daga baya sai suka samu labarin akwai wani mai farcen susa ‘Dan wani tsohon shugaban kasa, wani lokaci da ya gabata, wanda ya yi uwa ya yi makarbiya aka mayar da aikin cikin Makabarta, makaranta da kuma gidajen jama’ar wannan yankin,
Kamar yadda Alhaji Lawan wanda ya jagoranci mutanen garin ke shaidawa wakilin Jaridar Raihana da ya ziyarci Garin daidai lokacin da abin ya faru.
Yana mai cewar, mutanen garin masu bin doka da oda ne, kuma masu biyayya ga magabata ne musamman gwamnati.
A don haka yace, a baya an baiwa wasu mamallaka gidaje da Gonaki shaidar da zasu karbi diyyar wuraren su da akace aiki ya biyo ta kansu, amma har yanzu ba’a biya mutanen hakkokin su ba.
Kwatsam rana tsaka akace an sauya inda za’ayi gabatar da aikin zuwa cikin Makabarta, makaranta, Gonaki da kuma gidajen jama’ar garin na Danzaki.
Jin hakan ne tasa muka tuntubi mai unguwar ‘Dan Kargo Malam Amadu Ibrahim ‘Danzaki a karamar hukumar Gezawa, inda ya tabbatar da faruwar lamarin, amma shima ya sake jaddada rokon sa ga Mai girma Gwamnan Kano akan wannan lamarin da suke zargin ba zai haifar da ida mai Ido ba.
Ya kara da cewar, yanzu haka mutanen garin basa iya yin bacci, basu da nutsuwa da kwanciyar hankali sakamakon jin za’a karbe musu Gidaje da Gonakin su.
A karshe ya roki Gwamnan kano da masu ruwa da tsaki akan wannan lamarin su dubi halin da mutanen garin ke ciki, su tausaya musu.
Shugaban karamar hukumar Gezawa Alh. Bala Mukaddas ta bakin kansilan mazabar Jogana Hon Arma ya’u Muhammad Danzaki yace, har yanzu karamar hukumar Gezawa bata samu labarin yin wannan aikin ba.
A don haka yace, basa goyon bayan yin wannan aikin a wajen da aka dawo dashi saboda wani mutum daya, gwara a mayar dashi inda aka auna za’ayi tunda farko a cewar sa.
A karshe dai wasu da kawo yanzu bamu fayyace sunan su ba, amma mun hango motar ma’aikatar kasa da safayo ta jihar kano, sun ziyarci inda za’ayi aikin sun hakur – kurtar da mutanen garin tare da yin alkawarin zasu mika koken su ga Inda ya dace.