Ɗan gidan Tinubu, Sheyi, ya yi buɗe-baki da ɗan gidan gwamnan Kano da sauran ƴan siyasa a Kano
Dan Shugaban Ƙasa, Seyi Tinubu, ya yi buda-baki tare da Musulmai a Kano, ciki har da Al- Amin Abba Kabir, ɗan gidan gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a ranar Litinin din data gabata.
Sheyi ya kuma kaddamar da shirin ciyar da marasa galihu da nakasassu a wani bangare na shirinsa na Renewed Hope Youth Engagement (RHYE) a masallacin Al-Furqan dake cikin birnin Kano.
Shugaban kasar ya kai ziyara gidan fitaccen dan kasuwan nan, Aminu Dantata, daga bisani kuma ya kai gaisuwar ban girma ga gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.
Taron buda-bakin na musamman ya samu halartar ba ‘yan jam’iyyar APC kadai ba, har ma na jam’iyyar NNPP, karkashin jagorancin shugabanta na jiha, Hashim Sulaiman Dungurawa.