Ƴansanda sun kama jami'an NDLEA biyu bisa zargin kisan wata budurwa a Kano
'Yansanda sun kama jami’ai biyu na Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) a jihar Kano bisa zargin harbi da kisan wata budurwa mai suna Patience Samuel, ‘yar shekara 19, a unguwar Jaba.
Rahotanni sun bayyana cewa harbin ya faru ne a ranar Laraba da misalin karfe 10:55 na dare.
Majiyoyin sirri sun ce rundunar ‘yansandan jihar Kano ce ta kama jami’an.
Majiyoyin sun ce jami’an ‘yan sanda sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, suka kuma dauki Samuel zuwa Asibitin Koyarwa na Abdullahi Wase, inda aka tabbatar da mutuwarta.
An bayyana sunayen jami’an da aka kama da Nass Ridwan Usman, mai shekara 23, da kuma Sna Ismaila Yakubu, mai shekara 26.
Dukkansu suna aiki ne a hedikwatar hukumar ta NDLEA da ke Kano.
Majiyoyin sun ce ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike domin gano hakikanin dalilin harbin.