Ƴansanda sun kama wani mutum bisa zargin rushe gidan matarsa a Ekiti
Rundunar ƴansandan Jihar Ekiti ta cafke wani mutum mai suna Donald Fajuyi bisa zargin rushe gidan matarsa da katafila a kan titin Fajuyi da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar.
Wata mujalla da ke kawo rahotanni kan yaki da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi da sauran aiyukan rashin tsaro ta ruwaito cewa wanda ake zargin ya rushe gidan Bukola Fajuyi, matarsa, a ranar Lahadi, yayin da take a coci.
Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya kutsa kai gidan tare da wasu da ake zargin 'yan daba ne, inda suka yi amfani da babbar mota suka rushe ginin gaba daya tare da lalata kadarori masu daraja.