Ba a taɓa Sanatoci da yan majalisu yan amshin shata ba kamar na Majalisar ta 10 ba, sun zama "Rubber Stamp" sai yadda Tinubu yayi da su ~ Engr Kwankwaso
Kwankwaso ya bayyana haka ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda yace ya bi diddigin abubuwan da ke faruwa a Jihar Rivers cikin kwanaki biyu da suka gabata, kuma shirun sa na farko ya samo asali ne daga kokarinsa na ganin hukumomi da bangarorin da abin ya shafa sun yi abin da ya dace.
"Da farko, abin takaici ne yadda Shugaba Bola Tinubu ya dauki matakin kashin kansa na dakatar da Gwamna Similayi Fubara na Jihar Rivers, Mataimakinsa, da dukkan zababbun ‘yan majalisar dokokin jihar daga mukamansu.
"Majalisa na da hakkin sa ido kan ayyukan bangaren zartaswa ba wai kawai yin abin da suke so ba. Abin kunya ne ganin wannan Majalisa ta 10 ta zama yar amshin Shata fiye da kowace majalisa da ta gabata.
"Abin da ya fi damuna shi ne yadda bangarorin biyu na Majalisar Dokoki ta Kasa suka amince da wannan mataki na Shugaban Kasa ba tare da bin ka’idar da kundin tsarin mulki ya tanada ba.
"Tsarin mulki ya bayyana hanyoyin da ya kamata a bi wajen kada kuri’a kan irin wannan batun mai muhimmanci, amma yin amfani da kuri’ar murya (voice vote) wajen yanke hukunci akan wannan batu bai dace da hanyoyin da suka dace da gaskiya da adalci ba.
"Yadda aka gaggauta tattaunawa da yanke hukunci kan dokar ta-baci da ta rusa tsarin jagoranci na dimokuradiyya a Jihar Rivers ya raunana dimokuradiyyarmu.
"Bangaren shari’a yana da muhimmiyar rawar da zai taka wajen tabbatar da daidaito da adalci ga kowa. Ina da yakinin cewa ma’abota shari’a a Najeriya dole ne su farka su sauke nauyin da ke wuyansu, ta hanyar yin shari’a bisa gaskiya da adalci ba tare da wata alaka da karfin iko ba.
"A wannan matakin da dimokuradiyyarmu ta kai, wannan matakin da Shugaba Tinubu ya dauka na dakatar da dukkan zababbun shugabanni a Jihar Rivers ba wai kawai rashin bin doka ba ne, har ila yau yana iya haddasa rudani da rashin bin doka a gaba. Majalisar Dokoki ta Kasa, wadda ya kamata ta dinga sa ido a kan bangaren zartaswa, bai kamata ta mara baya ga wannan kuskure ba.
"Bugu da kari, mutumin da ke alfahari da kasancewarsa mai kishin dimokuradiyya bai kamata ya dauki matakin sanya sojoji cikin lamarin shugabanci ba. Wannan babbar barazana ce ga ci gaban da muka samu cikin shekaru 26 da muke tafiyar dimokuradiyya.
"Bola Tinubu ya san illar bai wa soja damar kusantar mulki, musamman bayan kokarin da Shugaba Olusegun Obasanjo ya yi na mayar da su barikinsu a lokacin da ya jagoranci kasar nan.
"Jawaban da Ministan Shari’a na Tarayya ya yi akan aiwatar da dokar ta baci, sun haifar da tsoro a zukatan mutane a jihohin da ba su tare da jam’iyyar da ke mulki a matakin tarayya. Wannan mataki wani sabon salo ne na shafar ikon jihohi da ba su da ra’ayi daya da gwamnatin tarayya.
"Ina da ra’ayin cewa halin da ake ciki a Jihar Rivers bai bada dama ga irin wannan fassarar da aka yi wa sashi na 305(1) na kundin tsarin mulkin Nigeria na 1999 ba.
"Wannan mataki ya saba wa kundin tsarin mulki, kuma idan ba a dakatar da shi ba, zai iya haifar da yawaitar rashin bin doka da al’adar yin hukunci bisa son rai." A cewar Kwankwaso