Ban yi mamakin amincewar majalisar taraiya kan dokar-ta-baci a Rivers ba saboda duk ƴan cin-hanci ne ~ Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce bai yi mamakin cewa majalisar dokoki ta kasa ta amince da ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas ba.
A ranar 18 ga Maris, Shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas saboda rikicin siyasa da ya ki ci, ya ki cinyewa a jihar.
TheCable ta rawaito cewa a wata hira ta wani shiri mai suna Untold Stories with Adesuwa, wanda za a watsa gaba daya a ranar Laraba, an tambayi Atiku ko yana mamakin yadda ‘yan majalisar tarayya suka hanzarta amincewa da bukatar shugaban kasa kan dokar ta-baci.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya zargi shugabancin majalisar dokoki da “cin hanci da rashawa,” yana mai cewa suna iya yin komai.
“Ban yi mamaki ba domin na san shugabancin majalisar yana da cin hanci. Ba na nadama kan hakan. Za su iya yin komai,” a cewar Atiku.