Ganduje ya bayyana hakan ne yayin taron karbar gamayyar kungiyoyin yakin neman zaben Atiku Abubakar, wanda suka dawo jam'iyyar APC, ta hannun mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibril, wanda aka gudanar a Abuja.
Ganduje ya jinjinawa Sanata Barau kan yadda yake kokari wajen shigo 'yan jam'iyyun adawa cikin APC.