Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya tabbatar da kafa wata haɗakar ‘yan adawa da nufin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis, 20 ga Maris, 2025, a Cibiyar Shehu Musa Yar’adua da ke Abuja.
Taron ya haɗa manyan shugabanni da masu ruwa da tsaki a siyasar Najeriya, inda suka tattauna batun ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas kwanaki biyu da suka gabata.
Da aka tambaye shi ko wannan haɗaka za ta zama babbar ƙungiyar adawa a zaɓe mai zuwa, Atiku ya amsa a taƙaice da cewa, “Eh.”Atiku ya tabbatar da haɗakar 'yan adawa don kawar da Tinubu a 2027
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya tabbatar da kafa wata haɗakar ‘yan adawa da nufin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis, 20 ga Maris, 2025, a Cibiyar Shehu Musa Yar’adua da ke Abuja.
Taron ya haɗa manyan shugabanni da masu ruwa da tsaki a siyasar Najeriya, inda suka tattauna batun ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas kwanaki biyu da suka gabata.
Da aka tambaye shi ko wannan haɗaka za ta zama babbar ƙungiyar adawa a zaɓe mai zuwa, Atiku ya amsa a taƙaice da cewa, “Eh.”