Dadumi-Dumi Allah ya yiwa Babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Kano a kan harkokin Radio Rasuwa
Allah yayi wa Abdullahi Tanka Galadanci Rasuwa kafin rasuwarsa ya riƙe Babban mataimaki na musamman ga Maigirma Gwamnan Kano kan harkokin Radio.
Tanka ya yi shura wajen tsage gaskiya komai dacinta, kuma kwararren masanin siyasa ce wanda ake masa lakabi da "Bokan Siyasa",
Siyasar sa ba iya Kano ta tsaya ba, ta hadar kasa Najeriya dama wasu sassan kasashen duniya.
Ƙwararren ɗan siyasa ne da ya yi shura kan magana a shirye-shiryen siyasa na gidajen Rediyo a Kano.
Zai ai jana'izarsa a yammacin wannan rana ta Laraba da misalin karfe 05:00pm, a unguwar Galadanci.
Muna Addu'ar Allah ya jikan sa yasa ya huta yasa Aljannar firdausi ce makomar sa tare da sauran magabantan mu Ameen