Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya soki dakatar da Gwamnan Jihar Ribas da 'Yan majalisar dokoki da Shugaba Bola Tinubu ya yi, yana mai cewa wannan matakin na iya bata wa ƙasar suna.
Yayin da yake jawabi a matsayin Shugaban Taron Gidauniyar Haske Satumari a Abuja a ranar Asabar, Jonathan ya ce ya ji takaici cewa an cire jami’an da aka zaÉ“a.
“Wadannan matakai da mahukunta a É“angarorin zartaswa da majalisa suka É—auka suna sanya Æ™asar cikin kallo mara kyau,” in ji shi.
Matsayinsa na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-É“aci a yankin mai arzikin man fetur na Kudu maso Kudu, sannan ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
Ya ce an É—auki wannan matakin ne domin dawo da kwanciyar hankali a jihar da ke fama da rikicin siyasa sakamakon rashin jituwa tsakanin gwamnan jihar da ‘yan majalisar dokoki.