Dambarwar masarautar Kano: Wajibi ne gwamnatin Kano ta bi hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke
Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Danagundi, ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ma duk wasu masu ruwa da tsaki da su bi hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke a kan dambarwar masarautar Kano a jiya Juma’a.
Kotun dai ta bayar da umarnin a dakata daga ɗaukar wani mataki har zuwa lokacin da kotun koli za ta yanke hukunci kan shari'ar.
Dan agundi ya yi magana kan hakan ne a Kano yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a fadar Nasarawa a yau Asabar.
Ya jaddada cewa dole ne dukkan bangarorin su mutunta hukuncin kotun, ciki har da hukumomin tsaro da ke da alhakin wanzar da zaman lafiya a jihar.
Aminu Dan agundi ya kuma shawarci Gwamna Abba Yusuf da ya mutunta hukuncin.