Fitaccen ɗan wasan Kannywood Baba Karkuzu, ya rasu
Fitaccen ɗan wasan fina-finan Hausa na Kannywood Abdullahi Karkuzu, wanda aka fi sani da Baba Karkuzu ya rasu yau Talata, a Asibitin Koyarwa na jami'ar Jos, bayan doguwar jinya da ya yi fama da ita.
Za'a yi jana'izarsa gobe Laraba da safe, a gidansa da ke titin Haruna Hadejia, a cikin garin Jos, jihar Filato.