Gobara ta tashi a safiyar wannan Larabar ta laÆ™ume kasuwar ’yan gwan-gwan da ke unguwar Dakata a Ƙaramar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano.
Kasuwar wadda ake kira da "Kwalema" tana nan a kan titin Zango, daura da gidajen man Dominion da kuma Mobil da ke makwabtaka da ofishin Hukumar WAEC yankin karamar hukumar nasarawa.
Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa jami’ansu na ci gaba da Æ™oÆ™arin kashe gobarar da ke neman wuce gona da iri.
Sai dai ya bayyana cewa duk da bincike ya soma gudana, amma kawo yanzu ba su gano musabbabin tashin gobarar ba.