Gobara ta tashi a kwalejin horas da jami'an Civil Defence a Katsina
Wata gobara da ta kama a cikin kwalejin horas da jami'an Hukumar Tsaro Ta Civil da ke cikin garin Katsina ta ƙone ɗakunan masu yawa da sauran kayayyaki.
Gobarar wadda ta fara ci ranar Litinin har zuwa Talata ta ƙone aƙalla ɗakuna uku da ɗakunan da ke kan bene, da katakai da rufin benen, tare da shafar wasu ɗakuna na kusa.
Ka zalika, gobarar ta ƙone kayan abinci da sauran wasu kayayyaki.
Kawo yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba, sai dai jami'in hulÉ—a da jama'a na hukumar, SC Buhari Hamisu ya shaidawa Alfijir Radio cewa ana kyautata zaton wutar lantarki ce ta haddasa ta.
Yayin ziyarar duba irin ɓarnar da gobarar ta yi bayan an kashe ta, kwamandan Hukumar Tsaro Ta Civil Defence a jihar Katsina, Aminu Datti Ahmad wanda ya samu rakiyar jami'an kiwon lafiya da magance afkuwar iftila'i ya bayyana ta a matsayin wani baƙon al'amari.
Ya sha alwashin haɗa hannu da jami'an kashe gobara na ƙasa da na jihar Katsina da kuma kwamandan kwalejin, ACG Babangida Abdullahi Dutsinma domin magance afkuwar irin lamarin a gaba.