Gwamna Yusuf ya karrama zakarun gasar karatun Alkur'ani tare da basu kujerun aikin Hajji
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karrama gwarazan gasar karatun Alƙur'ani mai girma a fadar gwamnati da ke Kano.
A wata sanarwa da Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya aikewa manema labarai a jiya Talata, gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin sa wajen ci gaban karatun Alkur'ani mai girma.
A yayin taron, gwamna Yusuf ya sanar da daukar nauyin karatun gwarazan su biyu, Gwani Sunusi Abubakar mai shekara 17 da Gwana Fatima Abubakar zuwa Jami'ar Al-Azahar da ke Egypt.
Baya ga haka, ya baiwa su biyun kujerun aikin Hajji da kyautar filaye da kuma kyautar kuÉ—aÉ—e.
Gwarazan Æ´an asalin jihar Kano ne, inda Gwani Sunusi Abubakar ya fito daga karamar hukumar Gezawa ya samu nasara a matakin kasa tare da Gwana Fatima Abubakar wadda itama ta samu nasara a matakin kasa.
Sauran wadanda su ka zo na biyu da na uku su ma sun samu kyautar Naira miliyan 1 da kujerar aikin Hajji ko wannensu.