Gwamna Yusuf ya yi barazanar ƙwace gidaje a biranen Kwankwasiyya da Amana da Bandirawo idan masu su ba sa amfani da su
Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya bai wa masu gidaje a biranen Kwankwasiyya, Bandirawo, da Amana wa’adin fara zama a gidajensu ko kuma su fuskanci soke mallakarsu.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Rabi’u Kwankwaso, ne ya kirkiri wadannan birane a lokacin wa’adin mulkinsa na biyu.
Da yake jawabi a ranar Litinin a gidan gwamnati, yayin rantsar da Ibrahim Yakubu a matsayin sabon kwamishinan gidaje Gwamna Yusuf ya bayar da wa’adin zuwa watan Yuni 2025 domin masu gidajen su yi amfani da su.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta fara gyaran gidajen a wadannan unguwanni domin a yi amfani dasu yadda ya dace.
A cewar sa, gwamnati na aiki don dawo da martabar garuruwan ta hanyar gyara tsarin da aka tsara tun farko.