Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jaddada aniyarsa na inganta rayuwar marayu a Kano ta hanyar samar da ingantattun ababen more rayuwa da shirye-shiryen da zasu samar da walwalar jama’a.
Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne yayin bude baki da aka shirya tare da marayu a Fadar Gwamnatin Kano.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna, Mustapha Muhammad, ya fitar a ranar Lahadi.
Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa marayu cewa gwamnatinsa za ta tallafa musu wajen samun ilimi mai zurfi a jami’o’i ko kuma wasu cibiyoyin ilimi.
Sannan Gwamnan ya yi alkawarin tafiya aikin Hajji da wasu daga cikin Marayun na Kano a wannan shekarar.
"Uba gare ku, Gwamna, shi ne Amirul Hajj. Dole ne in tafi da wasu daga cikinku. Wannan farkon farawa ne," in ji shi.
Tun da farko, Kwamishiniyar Harkokin Mata, Yara da masu bukata ta mussaman, Hajiya Amina Abdullahi, tare da Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, da Shugaban Ma’aikata, Alhaji Abdullahi Musa, sun yaba wa Gwamna Yusuf bisa yadda yake nuna kulawa ta musamman da sadaukarwa ga marayu.