Gwamnatin Kano ta sha alwashin biyan ma'aikatanta kafin Bikin Karamar Sallah
Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar wa ma’aikatan gwamnati a jihar cewa za'a biya su albashinsu kafin bukukuwan Eid-el-Fitr, (idin Karamar sallah) wanda ake sa ran zai fara daga ranar 25 ga Maris.
Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Faruk Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin.
An shirya taron manema labarai ne domin sanar da al’umma matakan da gwamnatin jiha ke dauka don gujewa matsalolin da aka fuskanta wajen biyan albashin watan Fabrairu.
Yayin da yake jawabi a taron, Alhaji. Umar Faruk Ibrahim ya bayyana cewa gwamnati na sane da bukukuwan Sallah karama, da ke karatowa, kuma za ta tabbatar da biyan albashin watan Maris kafin bikin.
A cewarsa, ma’aikatan gwamnati a jihar za su tabbatar da sahihancin albashinsu na watan Maris kafin a biya su, domin gujewa matsalolin da aka fuskanta a baya.
Alhaji. Faruk Ibrahim ya bayyana cewa wannan mataki ya zama dole sakamakon korafe-korafen ma’aikata kan matsalolin da suka hada da cire kudade daga albashinsu na watan Janairu da Fabrairu.
Ya kara da cewa an umarci ma’aikata ta hannun ma’aikatunsu da hukumomi (MDAs) da su tabbatar da bincikar jerin sunayensu da albashin da aka rubuta musu, tare da sanar da duk wata matsala da suka gano domin daukar matakin da ya dace.
Har ila yau, ya bayyana cewa za’a manna sunayen ma’aikata da albashinsu a wurare da suka dace a cikin ma’aikatu da sakatariyoyin kananan hukumomi 44 na jihar domin saukaka aikin tantancewa.
SSG ya kuma bayyana cewa an kafa kwamiti domin duba matsalolin da aka samu wajen biyan albashin ma’aikatan gwamnati.