Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranakun hutun bukukuwan Sallah
Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 31 ga Maris, da Talata, 1 ga Afrilu, 2025, a matsayin ranakun hutu don bukukuwan Ƙaramar Sallah bayan kammala azumin Ramadan.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, inda ya taya al'ummar Musulmi murna bisa nasarar kammala azumin watan Ramadan.
Cikin wata sanarwa da babban Sakatare na Ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, ya rattaba wa hannu, Ministan ya aike da fatan alheri ga Musulmi tare da yin kira da a ci gaba da aikata halaye nagari da aka koya a cikin Ramadan – kamar hakuri, tausayi, kyautatawa, da zaman lafiya.