Gwamnatocin Kano, Bauchi, da Kebbi sun bayyana cewa ba za su sauya matsayar rufe makarantu cikin watan Ramadan ba
Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta nuna damuwa kan rufe makarantun a lokacin azumi.
Gwamnatin Kebbi ta ce an yanke hukuncin ne bayan tuntubar shugabannin addinai, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki, Bauchi da Kano sun jaddada cewa hutun Ramadan na cikin tsarin shekarar karatu, kuma ba zai kawo cikas ga dalibai ba.
Gwamnatocin jihohin Kano, Bauchi da Kebbi sun tabbatar da cewa hutun Ramadan da aka bai wa makarantun firamare da sakandare zai ci gaba da kasancewa kamar yadda aka tsara.
Har zuwa lokacin cikar wa'adin hutun da gwamnatocin suka diba.