Hadakar Atiku da El-Rufai da Obi ba za ta iya kayar da APC ba ~ Shekarau
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa babu wata haÉ—akar ‘yan siyasa da za ta iya sauke Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki a zaÉ“en 2027.
Matsayar Shekarau na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan wasu manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da É—an takarar shugabancin Æ™asa a jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, suka soki matsayar Gwamnatin Tarayya game da rikicin siyasa a Jihar Ribas a wani taron manema labarai da suka gudanar a Abuja.
A wata sanarwa da Dr. Sule Yau ya fitar a madadin Shekarau, ya jaddada cewa, sabanin abin da wasu ke hasashe, wannan haÉ—aka kawai wata tarayya ce ta masu niyyar tsayawa takarar shugaban Æ™asa ko mataimakin shugaban Æ™asa, kuma babu wanda daga cikin jagororin wannan haÉ—aka da ya tuntubi shugabancin jam’iyyarsa.
Sanatan ya bayyana haÉ—akar a matsayin wata hadin guiwa ta wasu gungun mutane kawai, yana mai cewa, ko da suna da manyan sunaye, hakan ba ya nufin sun haÉ—e wuri guda domin zama jam’iyya guda ba.
A cewarsa, “HaÉ—akar wasu manyan jiga-jigai daga jam’iyyun adawa abu ne mai kyau, kamar yadda aka gani kwanan nan a Æ™arÆ™ashin abin da suke kira ‘coalition’ na jam’iyyun adawa.
“Babu É—aya daga cikin manyan jagororin da ke tafe da shugabancin jam’iyyarsa. Kuma wannan taron wasu gungun mutane, duk da suna da manyan sunaye, ba za a kira shi ‘merger’ ba, domin a bisa doka, sai jam’iyyun da aka rijista ne kawai za su iya yin cikakken haÉ—aka.”