Hukumar EFCC ce ta tabbatar da kama Murja Ibrahim Kunya bisa zargin ta da watsa takaddun naira, hukumar ta ce ta kama ta ne a wani É—akin Otal É—in Tahir a jihar Kano.
EFCC ta ce ta kama Murja Kunya bayan da ta tserewa beli tare da gujewa kamun jami’an hukumar.
Tunda fari dai an kama Murja a watan Janairun 2025 sakamakon karya dokokin Babban Bankin ƙasar CBN.