Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da haramta kidan Gwauro, da ake fara gudanarwa a ranar 10 ga watan Azumin Ramadan.
Mataimakin kwamandan hukumar Sheikh Mujahideen Aminudden ne ya bayyana hakan, inda ya ce kiÉ—an gwauro ya asali ya samo daga masu bautar tsumburbura, sannan musulunci bai yadda da hakan ba.