Hukumar tace Fina-finai a Kano tace duk wanda yataka doka, doka zatayi aiki akansa a lokacin bikin Karamar sallah ~ E.S Abba El-Mustapha
Bazamu saurarawa duk wani gidan wasa ba idan ya sauka daga turbar addini ko al'adar hausawa ba a lokacin shagulgulan bikin Karamar sallah ba.
Zamu hukunta duk wani Gidan wasa da yabar masu shigar banza Ko ya hada maza da mata ko masu shaye-shaye a cikinsa a yayin shagulgulan bikin Karamar sallah
A kokarin ta na yaki da rashin da'a tare tsaftace yadda gidan wasanni da masu kidan DJ zasu gudanar da shagalin bikin sallah a Jahar Kano, Hukumar tace fina-finai da Dab'i ta Jahar Kano karkashin jagorancin shugabanta Abba El-mustapha ta bayyana shirinta na saka kafar wando daya da duk wani gidan wasa ko mai kidan DJ aka samu da aikata yin rashin da'a a yayin gudanar da bikin sallah a Jahar Kano, inda Hukumar tace ta shirya wata tawaga ta musamman da zasu kewaya gidajen wasannin a ranakun sallah karkashin kulawar Alh. Abubakar Zakari Garun babba Daraktan Dab'i na Hukumar.
Tawagar wacce aikinta shine saka ido akan dukkannin gidajen wasannin a fadin Jahar hadi da masu kidan DJ zasu tabbatar ba'a bawa masu shigar banza ko shaye - shaye damar shiga gidajen wasannin ba haka kuma,
Haka zaluka Hukumar ta hana hada maza da mata a guri daya a yayin bikin sallar. Abba El-mustapha yace tawagar zasu rinka aiki ne babu dare ba rana a cikin sirri tare da bayyane tun a rana daya ga sallah har zuwa lokacin da za'a kammala bikin sallar domin cimma nasarar aikin da akasa a gaba.
Abba El-mustapha na Kara yin gargadi da kakkausar murya ga masu gidajen wasanni tare da masu sana'ar DJ dasu bi dokokin Hukumar sau da kafa domin gujewa fushin Hukumar. A karshe ya yi kira da iyaye dasu cigaba da kula da tarbiyar ya'yansu tare da addu'ar Allah yasa ayi bikin na sallah lafiya a gama lafiya