Jihar Kano ta samu sabon kwamishinan ‘yan sanda.
Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kasa, ta amince da nada Dr, Ibrahim Adamu Bakori, a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano.
Bakori dan asalin jihar Katsina, ya maye gurbin tsohon kwamishinan ‘yan sanda Salman Dogo Garba, wanda aka kara masa girma zuwa mukamin mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda.