Kafewar Dam din Yan Ganau dake Karamar Hukumar Tsanyawa a Kano na iya janyo asarar Miliyoyin Kudade sakamakon bushewar amfanin noma
Yanzu haka daruruwan manoma ne ke cikin fargaba, bayan da suka zuba milyoyin kudinsu da niyyar yin noman rani a kewayen dam din 'yan ganau dake karamar hukumar Tsanyawa, sai dai a yanzu haka dam din ya 'kafe.
Manoman wadanda suka ce ko rijiya da suke tonawa domin ban ruwa a yanzu haka, basa iya taras da ruwan saboda ya yi nisa gashi kuma masu karamin karfi ne balle su saka a yi masu riyojin burtsatse.
A yanzu haka masara da tumatir da sauran kayan lambu na milyoyin naira ne ke konewa saboda rashin ruwa a wannan waje.
Daya daga cikin manoman mai suna Rahamatullahi Abdussalam, ya ce suna kallo amfanin gonakin nasu ke bushewa babu yadda suka iya.
Manoman sunce ko a shekarar data gabata Sanatan Kano ta Arewa ya tura masu aiki zuwa dam din, amma daga karshe aikin ba'a yi shi yadda ya kamata ba.
A saboda haka manoman sunyi kira ga mahukunta a dukkanin matakai, kama daga shugaban karamar hukumar Tsanyawa da dan majalisar wakilai na Tsanyawa da Ghari da sanata Barau Jibrin da kuma gwamnan jihar Kano da su gaggauta Kai masu dauki domin ceto gonakin nasu daga bushewar da suke yi.