Kamfanin sadarwa na 9mobile ya karyata rade-radin cewa ya rufe aiyukan sa a Najeriya.
Hukumar gudanarwar Kamfanin na 9mobile ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a jiya Juma’a a Legas.
Kamfanin na 9mobile ya ce rahoton ba shi da tushe balle makama sai dan da nufin haifar da firgici a tsakanin masu amfani da layin sa.
"Mun fahimci cewa wasu kwastomomin mu kwanan nan sun fuskanci kalubale, musamman tare da Mobile Number Portability (MNP), sabis ɗin da ke ba da damar yin hijira zuwa wani layin.
"Muna so mu fayyace cewa 9mobile bai taba hana kwastomomin mu yin hijira zuwa wasu kamfanunuwan sadarwa ba," a cewar sa.
Kamfanin ya ce ya ci gaba da bin dokokin masana'antu, kuma ya himmatu wajen samar da ayyuka masu inganci ga kwastomomin sa.