Shugaban kasa Bola Tinubu ya roƙi gwamnoni da mambobin majalisar zartaswa ta tarayya da su mayar da hankali kan manufofi da albarkatu da za su amfani talakawa da marasa galihu a Najeriya.
Shugaban Æ™asar ya yi wannan roÆ™o ne a daren Litinin yayin Bude baki a fadar gwamnati da ke Abuja, inda ya karÉ“i bakuncin gwamnoni, Ministoci, shugabannin hukumomin tsaro, da shugabannin ma’aikatu, don yin buda-baki na Ramadan.
Tinubu ya yi magana kan muhimmancin jagoranci na kishin ƙasa, inda ya roƙi gwamnoni da su ɗauki kansu a matsayin shugabanni masu alhakin kai ƙasar zuwa tudun mun tsira.
Ya ce manufofin gwamnatinsa da suka mayar da hankali kan jin daÉ—in al’umma sun fara haifar da sakamako mai kyau.