Ku rungumi zaman lafiya domin ku ne da nasara ~ Sarki Sanusi ga masoya
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll, ya yi kira ga al’ummar jihar da su kasance masu bin doka da oda, su zauna lafiya, kuma su hada kai don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar.
Da ya ke jawabi a wurin taron buÉ—e-baki na musamman a fadarsa, Sarkin ya soki masu adawa da dawowarsa kan karagar mulki, inda ya bayyana cewa “wuta za ta cinye masu tayar da zaune tsaye a cikin birnin Kano.”
Sanusi ya kara da cewa, waÉ—anda ke kalubalantar sarautarsa na jayaiya ne da ikon Allah, inda ya ce za su “fuskanci sakamako mai muni a Æ™arshe domin sun bijirewa abin da Allah Ya Æ™addara.”
“Muna roÆ™on kowa ya kasance cikin lumana. Wannan lamari ne na nufin Allah, kuma Shi ba Ya bukatar taimakon kowa,” in ji Sarkin cikin harshen Hausa a wani bidiyo da TheCable ta gani.
“Muyi hakuri mu ci gaba da yin addu’a, domin Allah na tare da waÉ—anda ke kan hanya madaidaiciya.
“Wuta za ta cinye duk wanda ke son haddasa fitina a Kano. Allah Ya kare mu da al’ummarmu daga dukkan sharri. Mu ci gaba da zaman lafiya da kuma yin addu’a.
“Wanda ya Æ™alubalanci hukuncin Allah ba zai taÉ“a cin nasara ba.”
Jawaban Sanusi sun biyo bayan umarnin Gwamnan Kano, Abba Yusuf, na cewa majalisun masarautu su fara shirin Hawan Sallah.
Bayan haka, Aminu Ado Bayero, tuɓaɓɓen Sarkin Kano, shi ma ya sanar da hukumomin tsaro shirinsa na gudanar da Hawan da kuma bikin cika shekaru biyar a matsayin Sarkin Kano.