Kundin Tsarin Mulki Bai bai wa Shugaban Kasa Ikon Cire Gwamna, Mataimakinsa Ko 'Yan Majalisa ba da sunan Dokar ta bacci ~ Kungiyar Lauyoyi NBA
Kungiyar Lauyoyin Nigeria tace Shugaban ƙasa Bola Tinubu bashi da ikon da zai iya cire Gwamnan jihar Rivers, Sannan Kungiyar lauyoyin Najeriya ta bukaci Majalisar Dattawa ta ki amincewa da bukatar Tinubu.
A ranar 18 ga Maris, 2025, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar taɓaci a Jihar Rivers, yana mai dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, da dukkan 'yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
Wannan mataki ya biyo bayan rahotannin lalata bututun mai da wasu 'yan bindiga suka yi, tare da rashin daukar mataki daga gwamnatin jihar.
A martaninsu, Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta bayyana cewa dakatar da gwamna da sauran jami'an da aka zaɓa ba bisa ka'ida ba ne, kuma ya saba wa tanadin tsarin mulki.
NBA ta jaddada cewa Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 bai ba wa Shugaban Ƙasa ikon cire gwamna ko 'yan majalisar jiha ba, ko da kuwa an ayyana dokar taɓaci.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga Majalisar Ƙasa da ta yi watsi kan amincewa da wannan mataki, tare da gargadin cewa hakan na iya zama barazana ga dimokuradiyya a ƙasar.
Bugu da ƙari, NBA ta yi tambaya ko rikicin siyasa a Jihar Rivers ya kai matakin da ya cancanci ayyana dokar taɓaci, tare da jaddada cewa irin waɗannan matsalolin ya kamata a warware su ta hanyar tsarin shari'a da doka, ba tare da take haƙƙin dimokuradiyya ba.
A karshe, NBA ta yi kira ga duk masu ruwa da tsaki, ciki har da kotuna, kungiyoyin farar hula, da al'ummomin duniya, da su sa ido kan abin da ke faruwa a Jihar Rivers domin hana cin zarafi da take haƙƙin dimokuradiyya.