Kwamishinan kula da harkokin Tsaro da al'amuran cikin gida na Kano ya a jiye aikin sa
Kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida Manjo Janaral Muhammad Inuwa Idiris mai ritaya ya ajiye aikinsa.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana hakan, inda yace gwamna Abba ya kadu da ajiye aikin da kwamishinan yayi, Ya kuma mika sakon godiya sosai abisa gudun mowar da ya bayar.
Tuni gwamna Yusuf ya karbi takardar ajiye aikin na kwamishinan tsaron nan take. Wanda kuma kwamishinan bai bayyana dalilansa na ajiye aikin ba