Majalisar malamai ta ware dokoki Biyar da masu wa'azi yakamata su mayar da hankali kan su a watan Ramadan
Shugaban majalisar malamai ta Arewancin Najeriya, Malam Ibrahim Khalil, ya ce abu ne mai kyau a duk lokacin azumin Ramadan, masu wa’azi su riÆ™a kallon yanayin da al'umma suka samu kansu a ciki, wanda hakan zai sa su mayar da hankali kansu a lokacin tafsirin karatun Alqur'ani.
Malam Khalil ya ce a bana majalisar malamai na bukatar a mayar da hankali kan abubuwan biyar a yayin wa’azi.
1. Nu nawa Yan kasa muhimmancin shugaba.
2. Sanyawa Yan kasa kishin kasar su.
3. Zaburar da shugabanni sannin nauyin da ke kansu
4. Nunawa Yan siyasa illar cin mutuncin juna a kafafen yada labarai dama shafukan sada zumunta.
5. Sai kuma su kansu Malaman suyiwa kansu fada domin gujewa yadda Yan siyasa ke amfani da su wajen cimma bukatun su
Daga karshe sunyi fatan wannan wata na Ramadan zai zama silar samun sauki da rangwanme na matsi da al'ummar kasa ke ciki.